Apapa
Apapa Karamar hukuma ce da take a yammacin tsibirin Lagos a Jihar Lagos, Nijeriya. A cikin Apapa akwai tashoshin jiragen ruwa da dama kuma suna gudanar da ayyukansu a karkashin Nigerian Port Authority (NPA) wanda suka hada da aininhin tashar jiragen ruwa na Lagos da kuma tashar Lagos Port Complex (LPC).[1]
Apapa | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jihohin Najeriya | jahar Legas | ||||
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Apapa (en) | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 217,362 | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Southwest Nigeria (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 101252 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Bayani
gyara sasheKaramar hukumar Apapa tana nan kusa da tafkin Lagos (watau Lagos Lagoon), sannan kuma akwai nau'ikan kaya kala kala kaman kwantenoni da cargo-cargo, gidaje, ofisoshi da wata tsohuwar titin jirgin kasa wacce bata aiki a yanzu a arewacin Apapa. Itace kuma ainihin kafar shigo da kayayyaki na Najeriya har zuwa 5 ga watan Mayun shekara ta 2005 lokacin da ta koma karkashin kungiyar sufuri ta ruwa watau Danish firm A. P. Moller-Maersk Group. [2]Sannan daura da wannan tashar akwai tashar jiragen ruwa na Tin Can Island Port (TCIP).[3]
Har wayau akwai matatan man-fetur a cikin Apapa kamar Bua Group. Sannan akwai ofisoshi manymanya na kasuwanci sufurin kaya zuwa wurare daban daban a duniya. Daga cikin sanannun gine-gine akwai Folawiyo Towers. Acikin Apapa akwai hedikwatoci da dama kamar hedikwatan gidan jarida na Najeriya watau Thisday.[4]
Tarihi
gyara sasheAn tsinci wani sarakar tagulla a karni na 16 wanda a yanzu haka yana nan a jiye a gidan tarihi na British Museum. Acikin shekara ta 2015 aka kaddamar da aikin ginin gidajen zamani a fili me fadin eka 1000. An kammala aikin ginin a tsakanin shekarun 1957/1958 kuma ta wanzu tare da fadada Apapa Wharf. Gidajen sun kunshi tarin ma'aikatan kamfanoni musamman na gine-gine da sauransu. Makarantar German School Lagos tana Apapa a da.[5]
Gidajen da kayan Gwamnati
gyara sasheGidaje da wuraren karatu
gyara sasheA cikin Apapa akwai gidaje iri-iri kama daga na alfarma masu tsada har da matsakaita tsada da saukin kudi.[6]
Akwai wuraren shakatawa iri-iri kamar wurin hawa jirgin ruwa na zama a Apapa Creek.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Our Ports - NPA". nigerianports.org/. Nigerian Port Authority. Retrieved 12 September 2015.
- ↑ "Tancott, G (19 January 2015). "16 new RTG cranes for APM". Transport World Africa. Retrieved 12 September 2015.
- ↑ "Dredging for Contaienr Terminal in Apapa". Dredging Today. Retrieved 12 September 2015
- ↑ "Contact Us Archived 13 November 2011 at the Wayback Machine." Thisday. Retrieved on 16 November 2011. "THISDAY LIVE, 35, Creek Road, Apapa, Lagos, Nigeria"
- ↑ Okin, Isaac Abodunrin (1972). The urbanization process in the developing countries: a case study of Lagos, Nigeria (Thesis thesis).
- ↑ Home page. German School Lagos. 2 March 2003. Retrieved on 18 January 2015. "Beachland Estate Ibafon, Apapa, Lagos Nigeria"