Fulani

Wata ƙabila ce a najeriya wacce take a Afrika ta yamma

Fulani ko Fulata (tilo: Bafulatani ko Bafillace) Mutane ne da ke a Yamma Maso Arewacin Afrika tun a tsawon lokaci. Mafi shaharar sana'ar Fulani ita ce kiwon dabbobi da kuma sayar da nono[1], kuma suna tatsan nonon dabbobinsu domin sayarwa, Fulani wasu mutane ne da ke da kyakkyawar fahimta, a cewar 'yan uwansu da zamantakewar su sukan zauna da kowace ƙabilu lafiya kuma har su ƙulla aure a tsakaninsu amma mu a kasar Hausa da suka zo bamuga alkairin su ba domin datashin hankali suka farwa Hausawa ta hanyar kashe su musulmai sarakuna da sauran al'umma wanda danfodiyo ya jagoranta. Kiɗiddiga ta nuna cewa akwai Fulani aƙalla miliyan talatin da biyar a Najeriya.

Fulani

Yankuna masu yawan jama'a
Sudan, Sudan ta Kudu, Burkina Faso, Laberiya, Gambiya, Muritaniya, Najeriya, Nijar, Cadi, Mali, Kameru, Ghana, Saliyo, Togo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Ivory Coast, Guinea-Bissau, Benin, Gine, Habasha da Eritrea
tsohuwar (Nayejo) fulani dauke da kwarya nono
wata matar Fulani tare da yaran ta sun kewaye ta, tana wanke-wanke
Fulani
Rugar fulani
kalan shigar fulani
Rawan fulani
sun dugara dakiwun shano
rugan fulani
Fulani da shanun su.
Fulani suna tashi sun ɗora yaransu a kan jaki.

Harshe ko yaren da kuma Fulani suke magana da shi sunansa Fulfulde. Haka ake kiran sa a ƙasashen Najeriya da Nijar da Sudan da Kamaru, amma a tushen inda suka fito, watau kamar ƙasashen Senegal da Mauritaniya da Gini da sauransu. Ana kiran harshen da Pulaar' ko Fula.

 

ASALIN KALMAR FULANI

gyara sashe

Da fari dai, masanin ya faɗa cewar tabbataccen tarihi shi ne wanda ya zo a Alkur'ani da Hadisai, amma duk wani abu wanda ba shi ba kan iya zamowa gurbatacce, don haka bai doru a kan cewa wajibin duk abinda ya faɗa shi ne na gaskiya ba.


 
gidan fulani

A cewar sa asalin sunan Fulani shi ne Tuta (Futa Toro), kuma suna cikin tsofaffin ƙabilun duniya ne. Shi sunan Futa ɗin sun samo shi ne daga kakansu/uban su da ake kira Futa, kuma shi jika ne ga Annabi Nuhu. Ta wajensa aka samar da Samudawa da Adawa, don haka faɗin Allah Ta Ala a Alkurani (IRAMA ZA TUL IMAAD) da ƙabilar su yake, domin an samu cewa an taɓa kiran su da suna Iramawa.


Daga bisanin saboda yawaitar su ga yaƙe-yaƙe, sai aka dinga kiransu da suna Fatah, ma'ana Jarumai. Sannu a hankali kuma aka koma ambaton su da suna Futa.


Yanayin zaman su a wurare kuwa shi ne silar sauyawar sunayen su, ta yadda ake kiran wasu Futa Toro, ma'ana Futawa mazaunan Toro, da Futa Masina da Futa Jallo da Futa Falgo da sauran su


A cewar masanin, shi wannan sunan na FULANI, ya samo asali ne a Yammacin Afirka, sanda suka haɗu da ƙabilar MANDINKA wajen zama, waɗanda su ma kusan Fulani ne a halaye da dabi'u.


Malam Ahmad ya tafi a kan cewa Fulani kabilar farko ce da suka soma zaman Afirka, kuma su ne suka zo da addini Yammacin Afirka, amma fa addinin Yahudanci. Shi kuwa kowa ya sani addini ne na jinsi, ba na kowa da kowa ba.


Don haka idan Fulanin sun tara 'ya'yansu, su kan sanar musu da cewa 'Ana Hulbe (Fulbe) Allah'. Ma'ana mu masu tsoron Allah ne, kada kuyi abinda Mandinkawa abokan zamanmu suke aikatawa. Daga nan sai mandinkawa masu zuwa ganin su suka rinka kiransu da suna Fulah, kafin daga bisani sunan ya rinka sauyawa zuwa Fullata, da Fulbe.


ASALIN BAFILLATANI MAHANGA TA ƊAYA


Malam Ahmad ya sanar mana da cewa Bafillatani ya samu ne daga Annabi Nuhu A S.


Asalin zuriyarsa kuma a yankin Ɗurisinin dake da zama. A nan ne har Annabi Musa A.S ya riske su a zamaninsa lokacin da aka saukar masa da Attaurah. A lokacin suna masu bautar shanu, don haka sai ya kira iya ƙabilar sa Bani Israila zuwa bautar Allah makaɗaici.


Shi ya sa sai Bani Isra'ila suka yi kwaɗayin a sanya musu abin bauta kamar yadda Futawa suke yi, har kuma Musa Samiri ya shagaltar da su tare da sanya musu ɗan maraƙi a matsayin abin bautar Annabi Musa A .S.


Sai daga baya Annabin Allah Musa ya gane lamarin, sannan ya kira shugabansu mai suna Tori ya ƙarbi addini, shi ne har aka yi bikin karɓarsa ranar Asabar a jikin dutsen durisina. Fulani na kiran bikin 'Larki'. Har kuma sukan ce "RaduTori Sinin", watau ga Inda Tori ya musulunta wajen nuni da Ɗurisinin.


A wannan zamanin, sai ƙabilar Futah ta kasu. Wasu suka karɓi addinin Annabi Musa bisa biyayya da shugaban su Tori, wasu kuma suka bijere, inda suka yi Hijira zuwa Afirka ta Kudu, daga jikinsu ƙabilun Chusi da ake kira Totsi yanzu suka fita, da sauran ƙabilun da suka mamaye yankunan.


ASALIN BAFILLATANI MAHANGA TA BIYU


Aka ce asalin Fulani tare da Yahudawa suke da zama. Don haka kusancin su ke sanyawa ake kiransu da sunan Yahudawa. Kuma su mayaƙa ne marasa tsoro, waɗanda ba sa rabo da makami, sannan suna matuƙar ɗaukaka ranar Asabar sama da sauran ranaku saboda tarayyar su da Yahudawa. Sannu a hankali suka famtsama yankin Afirka ta Yamma.


ASALIN FULANI MAHANGA TA UKU


Wannan mahangar kuma ta nuna cewa Fulani tsatso ne daga zuriyar Annabi Ayyuba A.S..

Aka ce a lokacin da ya zama dattijo yana wa'azi a gefen tekun Indiya, sai aka ba shi wata mace aure wadda ba ta son sa. Don hakan idan dare ya yi sai ta guje masa zuwa bayan daki, a can kuma sai sheɗan ya rinka zuwar mata yana tarawa da ita. A haka har ta samu rabon yaro namiji wanda baya magana da kowa.


Aka yi magana a kan yadda ta samu wannan yaro dube da rashin tarayyar ta da maigidanta, amma Annabi Nuhu ya ce a kyale ta a matsayin matarsa, daga bisani hakan ya cigaba da faruwa har ta sake haifar yarinya mace.


Don haka waɗannan mace da namijin da suka girma su ne suka fara amfani da yarensu sabo na Fulatanci.


Fannin tsarotsaro

gyara sashe

Kimiya da Fasaha

gyara sashe

Sifirin Jirgin Sama

gyara sashe

Sifirin Jirgin Kasa

gyara sashe

Daga cikin muhimman abincin Fulani akwai Fura.

Musulunci

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  NODES