Gona
Gona: Wani waje ne ko kuma wani fili ne mai GIRMA da manoma suke kebewa don aikace-aikacen noma. Kama daga noman tsirrai da kuma kiwon dabbobi da kiwon kifi, da dai sauransu. Ana amfani da kayayyakin aikin gona iri-iri kamar, fatanya, garma, Gatari Adda, sungumi da dai sauransu. Wani lokaci manoma ko kuma masu aikin gona suna fuskantar matsaloli, na rashin wadatattun kudin siyen kayayyakin aikin gona, Kamar: takin zamani da wadansu abubuwan Noma. Haka kuma manoma suna fuskantar kalubale dangane da matsalar ambaliyar Ruwa,[1] itama tana kawo musu cikas, haka kuma fari shima yana karya manoma.
gona | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | artificial geographic entity (en) , building complex (en) da group of structures or buildings (en) |
Amfani | farming (en) |
Mamallaki | Manoma |
NCI Thesaurus ID (en) | C48953 |