Karin magana

hikima a zance
(an turo daga Karin Magana)

Karin magana, magana ce ko zance da hausawa kan yi wanda ke dauke da hikima da basira da azanci a ciki, domin yin hannunka mai sanda da huce takaici a kan wani abinda aka yi maka mara dadi.

karin magana
literary genre (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na paroimia (en) Fassara, saying (en) Fassara da popular saying (en) Fassara
Bangare na small genre of folklore (en) Fassara
Hashtag (en) Fassara Quotes, quoteoftheday da quotes
Has characteristic (en) Fassara oral tradition (en) Fassara
Nada jerin list of proverbial phrases (en) Fassara

Masana Harshen Hausa sun fassara karin magana gwargwadon fahimtarsu.

Daga ciki akwai: Farfesa dangambo a shekara ta alif da dari tara arba'in da takwas (1984), da ya ce, “Karin magana dabara ce ta dunkule magana mai yawa a cikin zance ko kuma dan kalmomi kaɗan cikin hikima”.

“Karin Magana Tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaka tare da bayar da ma’ana gamsashshiya, mai fadi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki” Kenan idan aka lura sosai za a ga cewa shi karin Magana, magana ce dunkulalliya wacce ba kowa ne zai iya gane ta ba, in ba tare da an yi masa cikakken bayani ba. Amma yau da gobe da kuma yawan amfani da ita, musamman a zamunan da suka shude, da ake yawan tsoma ta a cikin zance, sai ya zama shi Bahaushe yana iya gane abin sa. Misali:- ana kuma iya yiwa mutumin da ba shi da tattali nuni cikin dan kalmomi marasa yawa, kamar a ce da shi, wannan abin da ka ke yi zai hana ka farcen susa. Ko kuma idan ana son yin magana game da wani abu mai amfani da kuma maras amfani. Kamar a ce idan an aikata abin, wani abu maras dadi zai faru da wanda ya aikata, to ana iya yi masa nuni ta hanyar cewa da shi, wannan abin ba zai haifar maka da da, mai ido ba. Da sauransu. Kowace daya aka dauka daga cikin wadannan karin magana guda biyu, za a tarar cewa maganganu ne dunkulallu, wadanda idan aka tashi farfasa su, za su ci guri mai yawa. Amma idan aka fade su da baki ko aka rubuta su, za a ji su ko a gan su gajeru, sannan kuma shi wanda ake magana da shi zai iya fahimtar abin da ake nufi.[1] Karin magana zance ne a dunkule ko a karye, wacce aka tsakaita ta, ta hanyar karya magana, wacce ake fada yau da gobe domin isar da sakon hikima da hankalta ga wanda aka fadamawa a cikin harshen Hausa.[2]  kamar a ce “ Karen Bana Shi ke Maganin Zomon Bana” ko “Ra’ayi Riga” ko “ Tafiya Sannu Sannu Baya Hana Kwana Nesa”. “ Abinda Babba Ya Hango Yaro Ko Ya Hau Rimi Ba Zai Hango shi Ba” ko a ce “Sara da sassaka ba sa hana gamji toho”.

Karin magana tana da banbanci da wasu hikimomin magana na hausawa kamar su habaici, zambo, Kirari, Take, wanda wadannan daban suke da karin magana,[2] Kuma karin magana wani nau’i ne na azancin magana da harshen Hausa, ba tare da ka tsawwala ma mutum ba ta sigar magana ko tsawaita masa ba a cikin zance, amman ta hanyar amfani da karin magana zaka isar da saƙo a sauƙaƙe ko a fahimce.

Sigar sauyi

gyara sashe

Karin magana takan zo a sigar tambaya, habaici ko kuma azanci, sannan takan zo a sigar misali kamar karin maganar da ake cewa “ Ina ganin Kura da Rana/ yaya zan yarda ta cije ni?” wannan karin maganar ta zo ne a sigar tambaya, amma ba a bukatan wanda aka gaya ma karin maganan da ya bayar da amsa, kamar yace eh! Ko A’ah!, amman zai iya bayar da amsar ta sigar mayar da baƙan magana ko raddi, misali “Mallam Musa yaga alamun cewa Mallam Shehu naso ya ara fatanyarshi yaƙi dawo masa da kayansa, sai ya ce ma Mallam Shehu “ Ina ganin Kura Da rana, Ta ya zan yarda ta cijeni?” ma’ana ba zai yarda Mallam Musa ya mai wayo ba ya ara fatanyar sa ya cuce shi ba, Shi kuma Mallam Shehu da yin karin maganan ya fahimci cewa Mallam Musa ya gane, amman tinda al’amari ne wanda ba a fili yake ba na cewar tabbas cutar shi zai yi ba, sai shi kuma ya mayar masa da baƙar magana, ta hanyar cewa “ ba kura ba ce zaki ne” kaga a nan kamar ya amsa ga tambayar karin maganan ne, amman kuma bada amsawa, a wannan misali amsa tamabayan karin magana ta sigar tambaya ba laifi ba ne, amman galibi ba a amsawa sai dai a amsa ta sigar bakar magana, zambo, ko habaici.

Karin Magana Mai Siffar Tambaya

gyara sashe

1-Ƙasa ta gudu ta je ina?

2-Ina ganin kura da rana ta yaya zan yarda ta cijeni?

Karin Magana Mai Siffar Misali

gyara sashe

1- Wanka da gari baya maganin yunwa.

2- Mushen tinkiya ta fi yankakken biri.

3- Na shiga ban dauka ba, bata fidda ɓarawo.

4- Wankan wuta sau guda ka yafa.[3].

Wasu Karin Magana

gyara sashe

1- Hadarin kasa, maganin mai kabido.

2- Gobara daga kogi.

3- Hakuri maganin  zaman duniya.

4- Ana kukan karaya ga mutuwa ta zo.

5- Kome nisan daji, da gari gabansa.

6-kwaɗayi Mabudin wahala

7-wayon waniƙiƙi.

8-Hankaka mai da ɗan wani naka

9-kowa ya yi ƙeta,kansa.

10-kome wato amarya,a sha manta.

11-baƙo taɓa,ɗan gari kaba.

12-kwaɗayi makas kare.

13-yaro ɗan kalgo ne,tun yana ƙarami ake lanƙwasa shi

14-Horo ba kisa ba ne, gyara hali ne.

15-wanda bai sha kashi ba,ba ya jin bari.

16-Kada ka yi shuka a idon makwarwa.

18-Idan ungulu ta biya bukata,zabuwa tafi da zancenki.

19-Masu abu da abin su,kura da kalla bin kitse.

20-Wasa da yaro shi ya kan kawo reni.

21-"yau a garin? In ji maƙi baƙo.

22-Idan kura na da maganin zawo, tayi wa kanta.

23-Da ma yaya lafiya kura,balle tayi hauka?

24-"Ribar Ƙafa,"kura tayi karo da kwaɗo.

25-Ya zama kura da guntun ƙiri.

26-Bahili ya fi kowa rowa.

Canjin sigar Karin Magana

gyara sashe

A karin magana ana cewa “ hadarin ƙasa, maganin mai kabido”  ida dan dambe ya furta hakan kamar ya na yiwa abokin takararsa habaici ne, kamar ya ce “sai ni hadarin ƙasa, maganin mai kabido”. [4]

Amfani da Hikima

gyara sashe
  1. Takaita doguwar magana.
  2. Nuni, gargadi, da fadakarwa cikin nishaɗi, sannan kuma a takaice.
  3. Bayyanar da kwarewa da fasahar Bahaushe wajen iya magana.
  4. Adon harshe. Abin da ake nufi da adon harshe a nan, shi ne cewa karin magana yana karawa zance kyau da kuma dadi.[5]
  • Kowane bakin wuta, da na shi hayaki
  • Komai tsufan zaki, ya fi saurayin kare
  • Komai jarabar bunsuru, ya kiyayi matar kura
  • Komai nisan jifa, Kasa zai faɗo

.......... . ..... . ....... ,. ....

  • Wuta da Aljanna duka na Allah ne. Inji mai sabo
  • Duk wanda ka gani a inuwa, ba ta can ya faro ba.
  • Idan ka ji wane, ba banza ba.
  • Taya taito, ya fi ban cigiya.
  • Rashin jini, rashin tsagawa.
  • Idan kaga ki gudu, sa gudu ne bai zo ba.
  • Da mai rai ake rikicin duniya
  • Aikin banza, antura agwagwa ruwa
  • The Hausa world of Rudolf Prietze : being the complete collection of the scholar in the Hausa and German originals and the English versionsISBN978-125-659-1OCLC950033236.
  • Ahmed, Umaru Balarabe,. The Hausa World of Rudolf Prietze being the complete collection of the Scholar in the Hausa and German originals and the English versions. Volume 2. Zaria. ISBN 978-125-653-2.OCLC 992986877.
  • Aminu, Alhaji Ayuba ashekara ta. (1998). Kacici-kacici. Dukku, Malam Bello., Mu'azu, Mohammed Aminu. (1. publ ed.). Maiduguri: Compaq Publ. ISBN 978-32300-4-2. OCLC 634309537.
  • Furniss, Graham. ashekara ta (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.
  • Dikko, Inuwa.a shekara ta (2006). Ruwan bagaja : wasan kwaikwayo. Zaria: Northern Nigerian Pub. ISBN 978-978-169-143-0. OCLC 232270270.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-09-19. Retrieved 2020-08-19.
  2. 2.0 2.1 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute.p. 70
  3. Skimner (1988),(p238,239 and p73)
  4. Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute.p. 73
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-09-19. Retrieved 2020-08-19.
  NODES
INTERN 6