Katsina, mai yiwuwa kalmar daga "Tamashek" (yana nufin ɗa ko jini) ko mazza (maza) tare da "inna" (uwa). Karamar hukuma ce kuma babban birnin Jihar Katsina, Arewacin Najeriya. Katsina tana da nisan kilomita 260 km (160 mil) daga gabashin Birnin Sokoto, da kuma kilomita 135 Km (84 mil) daga Arewa Maso Yammacin Birnin Kano, tana kusa da iyakar ƙasar Nijar.

Katsina_State_banner
taswirar jihar katsina
Katsina Emir
IBB Way
Katsina na dukko
KATSINA_STATE_INSTITUTE_OF_TECHNOLOGY_AND_MANAGEMENT_KSITM
katsina
hasumuyar katsina
Fayil:Steel rolling rund-about, IBB Way, Katsina.jpg
Steel_rol
National_Museum_Katsina_State_03
ling_round-about,_IBB_Way,_Katsina

An ƙiyasta yawan mutanen Dake cikin Birnin Katsina a shekare ta 2016 da kimanin mutum 429,000.[1]

Birnin ya kasance cibiyar noma da kiwo inda ake noman gyaɗa da auduga da fatu da gero da kuma dawa,[2] sannan har ila yau, akwai masana'antun sarrafa man-gyaɗa, da ƙarafa, sannan birnin ya kasance cibiyar kiwon dabbobi kamar su shanu, tumakai, awakai da kaji da sauransu

Mafi akasarin mutanen birnin Musulmai ne daga ƙabilar Hausa da Fulani.

Tsohon shugaban kasan Najeriya Umaru Musa Yar'Adua ya kasance babban mutum ne daga Katsina.[3]

Gwamna mai ci na yanzu a Jihar Katsina shi ne Aminu Bello Masari,[4] wanda aka rantsar a matsayin gwamnan jihar a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015, wanda ya gaji kujerar daga hannun Bar. Ibrahim Shema.[5]

Masarautar Katsina

gyara sashe

Fadar Sarkin Katsina wanda akafi sani da "Gidan Korau" wani katafaren gini ne da ke tsakiyar tsohon birnin na katsina. Fadar ta kuma kasance muhimmin alama na daga al'adu, tarihi da kuma ɗabi'ar Katsinawa. Kamar yadda tarihi ya nuna, Muhammadu Korau ya gina fadar a shekara ta 1348 CE, wanda ake tsammani cewa shi ne sarki musulmi na farko a Katsina. Wannan ne yasa ake kiran masarautar da Gidan Korau. Fadar na ɗaya daga cikin gidan sarauta mafi tsufa kuma na farko-farko, tare da masarautun Daura, Kano Zazzau. Masarutar zagaye take da ganuwa wato katangar gidan sarki wanda a yanzu babu ita. Kofar da ke isa zuwa masarautar ita ce 'Kofar Soro' sannan kuma kofar da ke bayan ta ita ce 'Kofar Bai' (babu ita a yanzu). Fadar sarkin a cikin masarutar wani ƙayataccen gini ne mai ƙirar salo na gargajiya.[6] Sarkin Katsina na yanzu shi ne Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, daga dangin sarakunan Fulani.

 
Fadar Sarkin Katsina
 
Gidan rodi

Birnin na zagaye da ganuwa mai tsawon kilomita 21 (mil 13) wanda ake tsammani an gina ta a ƙarni na 1100.[7] Kafin zuwan addinin musulunci, jagorar Katsina na musamman shi ne Sarki, wanda yake fuskantar kisa a duk lokacin da aka same shi baya mulki yadda ya kamata. Daga ƙarni na 17 zuwa ƙarni na 18, Katsina ta kasance cibiyar kasuwanci na Ƙasar Hausa kuma ta zamo mafi girma daga cikin ƙasashen Hausa Bakwai. Fulani sun mamaye Katsina a lokacin Jihadin Fulani a shekarar 1807. A shekarar 1903 ne, sarkin Katsina na lokacin Abubakar ɗan Ibrahim ya miƙa wuya ga mulkin Turawa, wadda ta ci gaba har zuwa samun 'yanci kai a shekarar 1960.

 
Katsina a shekarar 1911

A lokacin kasuwancin yankunan kusa da Sahara na Afurka, birnin ya kasance mai albarka kuma muhimmin cibiyar kasuwanci, kuma ana daukanta a matsayin mafi shahara ta fuskar cinikayya, kasuwanci da kuma baiwar sarrafe-sarrafe. Matafiyi ɗan kasar Jamus, Friedrich Hornemann ne bature na farko da ya fara isa birnin a ƙarni na 19.

Tarihin birnin dangane da ilimin boko ya samo asali ne tun daga farkon shekarun 1950, a yayin da aka gina makaranta ta matsakaita ta farko a arewacin Najeriya. Akwai manyan makarantu a yanzu wanda suka haɗa da jami'oi guda biyu, Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da kuma ta 'yan kasuwa wato Jami'ar Al-Qalam Katsina; sannan kuma akwai politakanik wato Hassan Usman Katsina Polytechnic da kuma Federal College of Education, Katsina.Har wayau, birnin gida ne ga shahararren masallacin karni na 18 wato Hasumiyar Gobarau, hasumiya mai tsawon mita 15 (50 ft) wanda aka gina da laka da itacen dabino.

Al'amarin Boko Haram na 2020

gyara sashe

A cikin watan Disambar shekarar 2020, aka yi garkuwa da yara 300 'yan makaranta a Kankara.[8] Amma daga bisani an maido da yara 344 mako ɗaya bayan hakan.[8] Ƙungiyar Boko Haram ta yi iƙirarin cewa ita ta aikata hakan, amma jami'ai sun nuna rashin amincewa da hakan kasancewa babu ƙungiyar Boko Haram a yankin.[9]

Manyan Makarantun Birnin Katsina

gyara sashe

Hotunan Manyan wuraren garin Katsina tare da Makarantu

gyara sashe

Manyan Wuraren Garin Katsina

gyara sashe

Manyan Wuraren Garin Katsina

gyara sashe

Labarin ƙasa

gyara sashe

Dangane da rabe-raben yanayi na Koppen, Katsina ta faɗa acikin yanayi na zafi wato semi-arid climate, wanda ake rubuta wa a takaice da BSh a taswirorin yanayi na duniya.[10]

 
karamar hukumar katsina

Ruwan sama

gyara sashe

Akwai ƙarancin ruwan sama a birnin Katsina, babu rikodin na ruwa kwata kwata a tsakanin watannin Nuwamba zuwa March.

Jadawalin Ruwan Sama na Birnin Katsina
S/N Code Shekaru Junairu Febreru March Aprelu Mayu Yuni Yuli Agusta Satumba Oktoba Nuwamba Disemba
1. 65028 1990 0 0 0 0 29.9 57.9 198.8 220.2 34.7 0 0 0
2. 65028 1991 0 0 10.8 12.2 73.5 58.8 71.5 109.7 21.1 1.4 0 0
3. 65028 1992 0 0 0 0 33.6 19.9 89.3 119.4 70.7 0.2 0 0
4. 65028 1993 0 0 0 0 4.5 42.3 69 94.5 51.7 0 0 0
5. 65028 1994 0 0 0 3.1 12.3 42.3 107.9 174.2 113.1 20.3 0 0
6. 65028 1995 0 0 0 10 30 70 80 120 80 10 0 0
7. 65028 1996 0 0 0 0 42.6 44.5 38.1 66.8 67.8 0 0 0
8. 65028 1997 0 0 7.2 9.5 89.5 30.4 91.1 153.7 56.5 8.3 0 0
9. 65028 1998 0 0 0 10.1 11.4 43.4 114.1 116.6 135.2 0.8 0 0
10. 65028 1999 0 0 0 0 4.2 22.4 149.2 89.8 132.3 18.4 0 0
11. 65028 2000 0 0 0 0 1.6 106.8 299.9 160.2 62.1 45 0 0
12. 65028 2001 0 0 0 16.9 83.9 110.8 176 240.9 70.6 0 0 0
13. 65028 2002 0 0 0 0 2.9 141.3 170.4 71.3 199.1 9.8 0 0
14. 65028 2003 0 0 0 4 52.8 57.2 118.2 275.5 75.1 16.4 0 0
15. 65028 2004 0 0 0 0 74.9 151.2 161.1 268.8 42 0 0 0
16. 65028 2005 0 0 0 14.8 18.4 83.2 173.7 216.1 194 50.4 0 0
17. 65028 2006 0 0 0 0 26.1 69.9 170.9 314.9 129.7 15 0 0
18. 65028 2007 0 0 0 6.2 84.9 135.2 117.4 314.9 45.5 0 0 0
19. 65028 2008 0 0 0 16.6 8.5 63.3 182.9 213.9 67.7 4.2 0 0
20. 65028 2009 0 0 0 0 95 57.9 96.5 123.3 38.3 29 0 0
21. 65028 2010 0 0 0 85.6 8.1 118.8 226.1 448.9 76.6 48.6 0 0
22. 65028 2011 0 0 0 0 38 149.2 116.6 180.6 67.3 8 0 0
23. 65028 2012 0 0 0 0 59.5 135.2 117.4 314.9 129.7 15 0 0
24. 65028 2013 0 0 0 42.4 36.7 103.2 89 274.7 107.6 10.2 0 0
25. 65028 2014 0 0 0 0 38.1 39.5 178.9 178.7 46.3 0 0 0
26. 65028 2015 0 0 0 0 0 89.1 178.9 274.7 46.3 9 0 0
27. 65028 2016 0 0 0 0 4.5 42.3 69 94.5 59.5 0 0 0
28. 65028 2017 0 0 0 10.1 11.4 62 114.1 16.6 135.2 0.8 0 0
29. 65028 2018 0 0 0 0 2.9 141.3 170.4 149.7 199.1 63.8 0 0
30. 65028 2019 0 0 0 11.6 8.1 118.8 232.7 359.1 98.6 26.6 0 0

Tushe: Hukumar Kula da Yanayi, Katsina (NiMET) 2021.

Yanayin zafi ko sanyi

gyara sashe

Yanayi na nufin yanayi na zafi ko kuwa yanayin sanyi na wuri

Katsina na da yanayi na zafi sosai, tare da watan Aprelu a matsayin wata mafi zafi na kimanin 40.8 °C ko kuma 105.4 °F, tare da yanayi na matsakaicin zafi (31.4 °C or 88.5 °F) acikin watan December.[11]

S/N Code Shekara Junairu Febrelu March Aprelu Mayu Juni Juli Augusta Satumba Oktoba Nuwamba December
1. 65028 1985 31.7 29.7 36.5 36.5 38.6 35.9 31.6 31.3 33.2 35.5 33.9 28.2
2. 65028 1986 38.9 34.7 37 40.2 39.2 37 31.5 31.4 32.2 35.4 33.3 37.4
3. 65028 1987 30.4 33.6 36 37.6 40.1 36.6 35.1 32.6 34.4 35.7 34.1 30.1
4. 65028 1988 28.4 32 36.7 39 39.2 35.3 31.9 29.5 31.9 34.3 33.7 28.5
5. 65028 1989 26 28.4 35.2 39.3 38.3 36.2 32.4 30.9 32.6 33.6 33.6 29.6
6. 65028 1990 32.2 30.1 33.5 39.9 38.1 36.7 31.7 31.4 33.9 36.7 35.5 34
7. 65028 1991 29.4 35.9 35.9 39 35.3 35.1 31 30.5 34.4 36.4 33.3 28.9
8. 65038 1992 29.1 30.1 36.4 39 36.5 35.6 31 30.3 32.4 35.7 31.5 30.2
9. 65028 1993 36.5 32.5 36.5 39.3 39.3 36.5 33.3 31.5 33.1 36.9 35.5 29.5
10. 65028 1994 29.5 31.6 38.2 38.7 38.9 35.4 31.8 29.5 31.4 34.1 32.3 27.4
11. 65028 1995 27.7 31 38.1 38.8 38.3 36.1 32.9 30.9 32.6 35.4 32.2 31.7
12. 65028 1996 32.1 34.8 37.6 39.3 38.3 34.5 33.6 30.3 32.3 35.3 31.2 31.8
13. 65028 1997 31.3 28.5 34.8 38.3 36.5 35.1 32.4 31.7 33.6 36.5 35.6 30.4
14. 65028 1998 29.4 33.5 33.9 40.2 39.3 35.6 32.1 30.8 31.6 34.9 34.9 30.6
15. 65028 1999 30.8 34 39 39.5 39.3 38.1 31.7 29.5 31.4 33.4 33.2 29.7
16. 65028 2000 31 28.6 35.2 40.5 39.6 35.3 31 31 32.9 33.8 33.8 29.6
17. 65028 2001 29.3 30.4 36.9 38 37.8 34.3 31.3 30 32 34.8 33.6 31.9
18. 65028 2002 26.3 31.6 37 39.8 40.8 36 32.5 31.1 32.2 32.4 33.8 31
19. 65028 2003 34.7 35.3 39.6 39.4 34.4 35.6 31.3 30.8 32.8 33.8 33.5 31.7
20. 65028 2004 32 29.9 40 39 36.5 32 30 33 36 34 33.9 31.9
21 65028 2005 13.4 19.4 22 24 25.2 24.2 22.7 21.6 22.3 20 16.2 14
22. 65028 2006 15 18.1 20 21.4 26 25 23.2 22 22.2 22 15 11.8
23. 65028 2007 12.8 13.6 18.3 22.7 24.4 23.8 21.5 20.3 20.5 17.6 13.3 10.7
24. 65028 2008 9.5 14.4 20 21.2 23.2 22.8 21.1 19.5 19.8 17.5 13.3 11.5
25. 65028 2009 11.1 14.2 19.2 23.4 24.2 22.4 22.4 21.1 22.1 21.5 14.6 13.6
26. 65028 2010 14.5 17 19.7 23.8 23.7 23.8 22 20.7 21.9 19.6 14.3 14.1
27. 65028 2011 13.3 17.9 17.5 22.3 24.7 23.8 20.6 20.5 21.2 21.2 16.1 12.2
28. 65028 2012 12.6 16.4 18.6 25.4 26.3 23.4 21.3 20.4 21.8 22.1 19.0 14.6
29. 65028 2013 30.7 34.3 39.8 37.8 38.8 35.6 32.5 29.9 32.8 34.9 34.9 31.1
30. 65028 2014 30.8 32.2 37.5 39.7 37.6 36.6 33.4 30.7 32.5 35.9 34.8 30.7
31. 65028 2015 28.2 35.1 36.1 37.5 40.3 37.4 33.4 33.1 32.5 35.9 33.3 36.1
32. 65028 2016 28.2 32.5 38.5 40.5 39 35.1 32.2 30.9 32.3 36.5 35.5 30.7
33. 65028 2017 27.8 31.6 37.5 39.5 39 34.7 31.9 31 32.9 35.7 34.1 30.2

Tushe: Hukumar Kula da Yanayi Reshen Jihar Katsina (NiMET), 2021.

Watan Janairu shi ne wata mafi sanyi a Katsina tare da kimanin 14.7 °C or 58.5 °F.

S/N Code Shekara Junairu Febrelu March Aprelu Mayu Juni Juli Augusta Satumba Oktoba Nuwamba December
1. 65028 1985 16 14.7 22.6 24.2 26.7 24.4 22.2 22.2 22.6 21 17.5 14.7
2. 65028 1986 12.7 18 23.4 26.2 26.6 25.2 21.9 21.8 22.2 20.8 17.9 12.8
3. 65028 1987 13.1 16.7 21.4 22.3 25.2 24.9 23.9 22.6 23.6 22.5 17.5 14.5
4. 65028 1988 14.4 16.4 21.6 26.6 24.5 24.5 22.7 21.2 22.3 19.6 16.2 13.5
5. 65028 1989 11.1 13.8 18.9 23.1 25.1 24.4 22.2 21.7 22.8 20.6 15.8 13.8
6. 65028 1990 15.5 14.3 17 25.7 25.7 25.1 22.4 25.8 23.4 21 18.1 17.4
7. 65028 1991 13.7 18.9 21.7 25.5 24.5 24.4 16.2 12.6
8. 65028 1992 12.5 13.9 21.9 24.4 25.1 23.7 21.4 21.1 21.6 20.3 16.5 12.7
9. 65028 1993 11.3 15 19.7 22.7 24.9 23.1 21.1 20.7 21.1 20.5 17.5 12.5
10. 65028 1994 12.5 13.5 19.5 23.7 24.2 22.1 20 19.1 19.6 20.7 13.5 10.5
11. 65028 1995 11.2 13 19.1 22.7 23.5 22.2 20.5 19.4 19.7 19.8 14 12.4
12. 65028 1996 11.4 14.2 18.7 20.8 22.3 20.6 20 18.8 19 18.7 11.8 12.2
13. 65028 1997 14 14.1 21.1 24.7 24.6 24 22.9 22.3 23.1 23.5 18.9 14.2
14. 65028 1998 13.7 17.5 18.6 25.8 27.7 24.5 23.1 21.8 22.3 21.3 16.9 13.3
15. 65028 1999 12.6 16 20.2 23.1 24.7 24.1 20.8 20.4 20.7 19 15.1 11.3
16. 65028 2000 13 11.2 16.7 19 24.3 23.5 21 21 21.9 19.9 14.1 11
17. 65028 2001 20.2 12.6 16.5 23 24.6 23.2 22 21 21.9 19.7 14.6 12.8
18. 65028 2002 11.7 13.5 20 25.6 26 24 22.1 21.9 22.3 19.8 13.9 12.8
19. 65028 2003 16.5 18.6 24.4 24 23.6 23.5 22.2 22.1 22.5 19.9 14.5 12.5
20. 65028 2004 16 17.5 25 25 24.2 22 21 22 20 17 14.7 12.3
21 65028 2005 13.4 19.4 22 24 25.2 24.2 22.7 21.6 22.3 20 16.2 14
22 65028 2006 15 18.1 20 21.4 26 25 23.2 22 22.2 22 15 11.8
23. 65028 2007 12.8 13.6 18.3 22.7 24.4 23.8 21.5 20.3 20.5 17.6 13.3 10.7
24. 65028 2008 9.5 14.4 20 21.2 23.2 22.8 21.1 19.5 19.8 17.5 13.3 11.5
25. 65028 2009 11.1 14.2 19.2 23.4 24.2 22.4 22.4 21.1 21.1 21.5 14.6 13.6
26. 65028 2010 14.5 17 19.7 23.8 23.7 23.8 22 20.7 21.9 19.6 14.3 14.1
27. 65028 2011 13.3 17.9 17.5 22.3 24.7 23.8 20.6 20.5 21.2 21.2 16.1 12.2
28. 65028 2012 12.6 16.4 18.6 25.4 26.3 23.4 21.3 20.4 21.8 22.1 19.0 14.6
29. 65028 2013 14.3 15.8 22.1 23.4 24.3 22.7 21.9 21 22.3 20.9 18.3 15.9
30. 65028 2014 14.3 16.7 21.7 25.8 25.8 26.7 24.2 22.1 22.3 20.7 18.2 14.2
31. 65028 2015 12.3 18.1 20.8 22.2 26.6 24.8 22.7 22.3 23.3 17.6 13.3
32. 65028 2016 13.5 16.5 24.2 27.1 26.8 24.9 23.2 22.2 22 22.3 18.7 13.1
33. 65028 2017 13.4 16.4 19.9 25 27.1 24.8 23.1 22.4 23.1 19.9 16.6 15.4

Tushe: Hukumar Kula da Yanayi Reshen Jihar Katsina, (NiMET) 2021

Sanannun Mutane

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. Katsina (State, Nigeria) - Population Statistics, Charts, Map and Location, on March 21, 2016.
  2. Katsina The Encyclopædia Britannica Online. Retrieved February 20, 2007.
  3. "Umaru Musa Yar'Adua | president of Nigeria". Encyclopædia Britannica. Retrieved 2018-12-03.
  4. "Buhari, Katsina governor meet inside Aso Rock". Punch Newspapers. Retrieved 2018-12-03.
  5. "Biography of Katsina former Governor Ibrahim Shehu Shema". Katsina Post. Retrieved 2018-12-03.
  6. "KATSINA EMIRATE COUNCIL". Retrieved 6 August 2015.
  7. Katsina The Encyclopædia Britannica Online. Retrieved February 20, 2007.
  8. 8.0 8.1 "Nigeria school attack: Hundreds of boys". BBC News. 2020-12-17. Archived from the original on 2021-02-28. Retrieved 2021-02-28.
  9. Giles, Christopher (19 December 2020). "Nigeria school kidnappings: Is Boko Haram responsible?". BBC.
  10. Climate Summary for Katsina.
  11. Yu Media Group. "Katsina, Nigeria - Detailed climate information and monthly weather forecast". Weather Atlas. Retrieved 2021-08-19.

jihar katsina tana da kananan hukuma 34

  NODES
COMMUNITY 1