Matan Annabi

Matan Annabi sha uku

Matan Annabi Ta tabbata a cikin nassoshi cewa Annabi Muhammad (S A W) ya aura mata 11 a tsawon rayuwarsa sai dai wasu ruwayoyin sun nuna matansa 13. A Musulunce da kuma duk wani Musulmin kwarai na gari ana kiran su da Ummahati al-Muminin (Larabci: أم ٱلْمُؤْمِنِين; ma'ana 'Uwar Muminai'/Iyayen muminai) ana ambaton su da wannan kalma a matsayin alamar girmamawa, wannan kalmar ta samo asali daga Alqur'ani yazo a cikin Suratul Ahzaab {{النَّبِيُّ أَوْلَى بِالْمُؤْمِنِينَ مِنْ أَنْفُسِهِمْ وَأَزْوَاجُهُ أُمَّهَاتُهُمْ وَأُولُو الْأَرْحَامِ بَعْضُهُمْ أَوْلَى بِبَعْضٍ فِي كِتَابِ اللَّهِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُهَاجِرِينَ إِلَّا أَنْ تَفْعَلُوا إِلَى أَوْلِيَائِكُمْ مَعْرُوفًا كَانَ ذَلِكَ فِي الْكِتَابِ مَسْطُورًا Aya-6.png}} haka kuma Allah madaukakin sarki yana cewa a cikin Alqur'ani { ﴿يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا ٣٢﴾ [الأحزاب:32.[1][2]

Matan Annabi
group of humans (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Ahl ul-Bayt
Depicts (en) Fassara Mata a musulunchi, women in the Qur'an (en) Fassara da female figures in the Quran (en) Fassara
Alaƙanta da Yaran Annabi
Matan Annabi

Annabi Muhammad (S A W) ya auri matarsa ​​ta farko, a lokacin da yake da shekara 25 wato Nana Khadija bint Khuwaylid Allah ya kara mata yarda. Sun zauna da ita tsawon shekaru 25 har sai da Allah ya mata rasuwa. Bayan mutuwarta a cikin shekara 619 AD, ya auri mata 10 a cikin sauran shekarun rayuwarsa. Daga cikin wadannan matan biyu suka haifa masa ‘ya’ya: Nana Khadijah da Nana Mariya al-Qibtiyya Allah ya kara yarda da su. Duk matan Annabi sun kasance zawarawa kodai wadda aka saka ko kuma wadda mijinta ya mutu, ban da Aisha bint Abubakar Allah ya kara mata yarda. Baban ta Abubakar bin Abi Quhafa shine Khalifah na farko bayan rasuwar Annabi Muhammad (S A W)

Rayuwar Annabi Muhammad ta kebanta da zamani guda biyu: Makka kafin hijira, birni ne a yammacin kasashen Larabawa, daga shekara ta 570 zuwa 622 Miladiyya, da kuma bayan hijira a Madina, daga 622 har zuwa rasuwarsa a shekara ta 632. Hijira tana nuni ne ga yawan hijirar Fiyayyen halitta Annabi Muhammad da Sahabbansa, wanda akwai hijira ta farko da ta biyu, ta farko itace wadda ysa umurci Sahabbansa da suyi hijira zuwa garin Habasha, sai ta biyu sun tafi garin Madina tareda da abokin sa Abubakar saboda zalunci da musulmi suka fuskanta daga kafiran Makka na wannan lokacin. Bayan wannan hijirar duk an daura aurensa sai biyu.

Matansa da Shekaran Auran su

gyara sashe
  1. Khadija Yar Khuwailid 595–619 Ta farko.Kuma kakar sharifai wacca annnabi yace baisami kamartaba
  2. Sawda Yar Zamʿa 619–632
  3. Aisha Yar AbuBakar c.623–632 Wacce yafi so. Yar Abubakar
  4. Hafsa Yar Umar 624–632 Yar
  5. Zaynab Yar Khuzayma 625–627
  6. Hind Yar Abi Umayya 625–632
  7. Zainab Yar Jahsh 627–632
  8. Juwayriyya Yar al-Harith 628–632
  9. Ramla Yar Abi Sufyan 628–632
  10. Raihana Yar Zayd 629–631
  11. Safiyya Yar Huyayy 629–632
  12. Maimuna Yar al-Harith 630–632
  13. Maria al-Qibtiyya 630–632

Rayuwarsa a cikin iyalinsa

gyara sashe

Annabi Muhammad (S A W) ya zauna da iyalansa a wasu kananan gidaje kusa da masallacin Madina. Kowanne daga cikin waɗannan gidaje ya kasance faɗinsa mita shida zuwa bakwai, sai kuma da tsayi goma (mita 2.3). Tsayin rufin ya kasance na wani matsakaicin mutum a tsaye. An yi amfani da barguna a matsayin labule don rufe kofofin. Kamar yadda aka ruwaito daga Anas bin Malik cewa: “Annabi ya kasance yana ziyartar matansa duka wato yana kewayawa su duka, dare da rana, kuma su goma sha daya ne. Na tambayi Anas, "Shin Annabi da ƙarfinsa ne?" Anas ya ce: “Mun kasance muna cewa an bai wa Annabi qarfin mutum talatin (maza). Kuma Sa’id ya ce daga Qatada cewa Anas ya ba shi labarin mata tara ya aura (ba goma sha xaya ba).

Duk da cewa matan Annabi (S A W) suna da matsayi na musamman a matsayin su na Uwayen Muminai, amma bai bar su su yi amfani da matsayinsa na Annabi ba wajen samun kulawa ta musamman a bainar jama’a.

Manazarta

gyara sashe
  1. Aleem, Shamim (2007). "12. Mothers of Believers". Prophet Muhammad(s) and His Family. AuthorHouse. p. 85. ISBN 978-1-4343-2357-6.
  2. Al Kur'ani 33:6
  NODES