Adamu Waziri

Ɗan siyasar Najeriya

Adamu Maina Waziri (an haifeshi ne a ranar sha hudu 14 ga watan Satumba shekara ta alif dari tara da hamsin da biyu 1952) an naɗa shi ministan harkokin ƴan sandan kasa aNajeriya a ranar shida 6 ga watan Afrilun na shekara ta dubu biyu da goma 2010, lokacin da muƙaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana sabuwar majalisarsa.[1]

Adamu Waziri
Minister of Police Affairs (en) Fassara

2010 - 2011
Ibrahim Lame - Omoniyi Caleb Olubolade
Rayuwa
Haihuwa 14 Satumba 1952 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Rayuwar farko da Karatu

gyara sashe

An haifi Waziri a jihar Yobe a ranar goma sha hudu 14 ga watan Satumba shekara ta alif dari tara da hamsin da biyu 1952. Ya yi karatun BSc da MBA a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Ya zama malami a jami'ar Maiduguri a shekara ta alif dari tara da saba'in da tara 1979.[1]

Mukamai a masana'antu masu zaman kansu sun hada da Babban Darakta, Hydro Quest Najeriya da Babban Jami'in Bogaru International. A gwamnati ya yi aiki a Hukumar Bayar da Lamuni ta Dalibai, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, sannan ya kasance mataimaki na musamman ga Ministan Noma, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa, Ko’odinetan shirin kawar da talauci na kasa da kuma Shugaban Hukumar Kare Hatsari. Ya kasance Babban Sakatare, Asusun Haɓaka Fasahar Man Fetur tsakanin shekara ta dubu biyu da biyar 2005 zuwa 2006.[1]

Waziri ya kasance ɗan takarar gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin jam'iyyar PDP a zaɓen 2007. Bayan zaben shugaban kasa Umaru Musa 'Yar'aduwa an naɗa shi ƙaramin minista a ma'aikatar noma da albarkatun ruwa ta tarayya.[2] A ranar 29 ga watan Oktoba ta shekarar dubu biyu da tokas (2008) aka saka shi a cikin wani sauyi na majalisar ministoci.[ana buƙatar hujja]Waziri ya kasance mamba ne a ƙungiyar (Good Governance Group) ƙarƙashin jagorancin Ken Nnamani wanda ya miƙa mulki daga Umaru Yar'Adua zuwa Jonathan.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 "Ministers - the Profiles". ThisDay. 7 April 2010. Archived from the original on 11 April 2010. Retrieved 2010-04-13.
  2. "Profiles of ministerial nominees (3)". People's Daily. Archived from the original on 2023-02-23. Retrieved 2010-04-13.
  3. Suleiman M. Bisalla (21 March 2010). "20 Ex-Ministers to Bounce Back". Daily Trust. Archived from the original on 24 March 2010. Retrieved 2010-04-13.
  NODES