Al-Baqir
Muhammad bn Ali ( larabci : محمد بن علي الباقر), wanda aka fi sani da al-Baqir ( wanda ya bude ilimi ) (677-733) shi ne limami na biyar daga cikin limaman shia. [1] Shi ne dan Ali bin Husayn ko Zayn al-Abidin kuma imam na farko wanda ya fito daga jikokin Muhammad da Hasan bn Ali da Husayn bn Ali . Musulmin Sunni da Shia suna matukar girmama shi saboda shugabancinsa, iliminsa da kuma ilimin addinin Musulunci a matsayin masanin shari'a a Madina . Bayan wafatin Ali bn Husayn (Imami na huxu), mafi yawan ‘yan Shi’ar sun yarda da dansa al-Baqir a matsayin imami na gaba; wasu daga cikinsu suka ce, wani dan imam Zayd bn Ali shi ne imami na gaba, kuma ya zama ana kiran sa da Zaidiyyah . [2]
Al-Baqir | |||
---|---|---|---|
712 - 733 ← Ali ibn Husayn - Jafar as-Sadiq → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Madinah, 8 Mayu 677 | ||
ƙasa | Khalifancin Umayyawa | ||
Harshen uwa | Larabci | ||
Mutuwa | Madinah, 26 ga Janairu, 733 | ||
Makwanci | Al-Baqi' | ||
Yanayin mutuwa | (dafi) | ||
Killed by | Hisham ibn Abd al-Malik (en) | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Ali ibn Husayn | ||
Mahaifiya | Fatimah bint al-Hasan | ||
Abokiyar zama | Farwah bint al-Qasim (en) | ||
Yara |
view
| ||
Ahali | Zayd ibn Ali (en) , Husain bin Ali bin Husain (en) da Abdullah bin Ali bin al-Hussein (en) | ||
Ƴan uwa |
view
| ||
Karatu | |||
Harsuna | Larabci | ||
Malamai | Ali ibn Husayn | ||
Ɗalibai | |||
Sana'a | |||
Sana'a | Liman da muhaddith (en) | ||
Imani | |||
Addini | Ƴan Sha Biyu |