Alton Stanley Tobey (Nuwamba 5, 1914 - Janairu 4, 2005) Ɗan wasan kwaikwayo Ba'amurke, mai zanen tarihi, mai zane-zane, mai hoto, kuma malamin fasaha.

Alton Stanley Tobey
Rayuwa
Haihuwa Middletown (en) Fassara, 5 Nuwamba, 1914
ƙasa Tarayyar Amurka
Mutuwa Mamaroneck (en) Fassara, 4 ga Janairu, 2005
Karatu
Makaranta Yale University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a painter (en) Fassara
Artistic movement history painting (en) Fassara

An haifi Alton Tobey a Amurka a ranar 5 ga watan Nuwamba, shekarar alif ɗari tara da goma sha huɗu 1914. Yana da shekaru 20 ya sami gurbin karatu a Jami'ar Yale; Makarantar Fine Arts. Bayan ya yi aikin soja, ya kammala karatun digirinsa na farko a Yale, kuma ya zama ɗaya daga cikin Farfesa. Ya zauna tsawon rayuwarsa a ƙauyen Larchmont, wani ɗan yanki na wani gari a Mamaroneck, gundumar Westchester, New York. Ya auri Roslyn Tobey, mai koyar da piano kuma mawaƙiya. Ɗansu, David Tobey, mai zane ne kuma mawaƙi. Tobey ya mutu a ranar 4 ga Janairu, shekarar dubu biyu da biyar dai-dai 2005, a gidan kula da tsofaffi a Mamaroneck, New York.

New York Times ta bayyana Tobey a matsayin "mai zane-zane, mai hoto kuma mai zane wanda fitattun abubuwan da suka faru da fuskoki suka rataye a gidajen tarihi, dakunan karatu, gine-ginen jama'a, ofisoshin kamfanoni da tarin masu zaman kansu". Tobey yana cikin ƙungiyar Kasuwancin Mawaƙa ta ƙasar Rasha a cikin mafi kyawun masu fasaha a duniya na ƙarni huɗu da suka gabata.

Manazarta

gyara sashe
  NODES
os 2