Babakar Niasse
Babacar Niasse (an haife shi a shekarar 1996), ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tondela ta La Liga 2 . An haife shi a Senegal, yana buga wa tawagar ƙasar Mauritania wasa.
Babakar Niasse | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Dakar, 20 Disamba 1996 (27 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Senegal Muritaniya | ||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai tsaran raga | ||||||||||||||||||||||
Tsayi | 195 cm |
Aikin kulob
gyara sasheNiasse ya kasance ɗan wasan tsakiya mai kai hari, amma ya canza zuwa mai tsaron gida kuma an san shi da tsayin daka na musamman. Ya kammala karatun matasa na Aspire Academy, ya shiga Eupen a shekarar 2015.[1][2]
A ranar 21 ga watan Agustan 2019, Niasse ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru 3 tare da kulob ɗin Tondela na Primeira Liga na Portugal.[3]
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheAn haife shi a Senegal, Niasse ɗan asalin Mauritania ne. Shi ne mai tsaron gida na zaɓen 'yan 17 na Senegal don gasar cin kofin Afirka na U-17 na shekarar 2011 .[4][5] An kira shi don ya wakilci babban tawagar ƙasar Mauritania don wasan sada zumunci a cikin watan Maris 2022.[6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Babacar Niasse: "Immédiatement, tomber m'a plu" - DH.be". dhnet.be. Retrieved 2017-02-25.
- ↑ "NIASSE Babacar › KAS Eupen". as-eupen.be. Retrieved 2017-02-25.
- ↑ "NIASSE É REFORÇO" (Press release) (in Portuguese). Tondela. 21 August 2019.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Jeux Africains 2015 : Babacar Niasse d' Eupen prêt à venir". seneweb.com. Retrieved 2017-02-25.
- ↑ "CAF U17: Song, dance as Rwanda make World Cup finals - Futaa.com". futaa.com. Archived from the original on 2017-02-26. Retrieved 2017-02-25.
- ↑ Bamba, Oumlbenina Mint (March 19, 2022). "Mauritanie - CAN : liste des joueurs pour les matchs amicaux".