Claude Makelele (an haifeshi ranar 18 ga watan Fabrairu 1973) ya kasance kocin Faransane sannan tsohon kwararren dan dan wasa ne wanda ke buga wurin tsakiya mai tare. Yanzu haka mai joraswane na gasar Super lig na kasar Greece wanda ke bada horo s kungiyar Asteras Tripolis. Ya kasance daya daga cikin yan tsakiya masu tare na kowane lokaci.[1] Makelele ya samu lambar yabo na zama dan wasa mafi kyau a tsakiya mai tare a gasar Premier, musamman a karnin 2004-05 FA Premier League, inda ya buga wuri mai mahimmanci a taimakon kungiyarsa ta Chelsea ta lashe gasar da maki 95. A gida kuma, lambar ta tsakiya mai tare anfi kiranta da suna wurin Makelele.[2][3] a rayuwar kwallanshi, wadda ta kare a kungiyar P. S. G, Makelele ya buga kwallo a Nantes, Marseille, Celta Vigo, Real Madrid da Chelsea. Yaci gasar lig a Faransa, Sifaniya, da Ingila, gami da gasar Zakarun Nahiyar Turai a shekarar 2001-02 lokacin yana Kungiyar Madrid.[4] Haka zalika, Makelele yana daya daga cikin jerin yan wasa 11 mafi kyau na FIFPRO lokacin yana Chelsea.[5] Haifaffen Zaire, Makelele yayi rayuwar kasa da kasa a Faransa tsawon shekaru 13, kuma yana cikin jerin yan wasan Kasar Faransa wadanda suka wakilci gasar cin kofin duniya na 2006.

Makelele
Rayuwa
Cikakken suna Claude Makélélé Sinda
Haihuwa Kinshasa, 18 ga Faburairu, 1973 (51 shekaru)
ƙasa Faransa
Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
Harshen uwa Faransanci
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Stade Brestois 29 (en) Fassara1990-1991123
  FC Nantes (en) Fassara1991-19971699
  France men's national association football team (en) Fassara1995-2008710
  France national under-21 association football team (en) Fassara1995-1996111
  Olympique de Marseille (en) Fassara1997-1998322
  RC Celta de Vigo (en) Fassara1998-2000703
  Real Madrid CF2000-2003940
  Chelsea F.C.2003-20081442
  Paris Saint-Germain21 ga Yuli, 2008-29 Mayu 2011981
 
Muƙami ko ƙwarewa defensive midfielder (en) Fassara
Nauyi 65 kg
Tsayi 174 cm

Bayan ya ajiye kwallo, Makele ya cigaba da aikin horaswa, ya horas da Bastia da Eupen, mataimakin mai horaswa na P. S. G da Swensea.[6]

Rayuwar farko

gyara sashe

An haifi Makelele a Kinshasa, Zaire. Ma'anar sunan Makelele yana nufin "Hayaniya" a yaren Lingala.[7], daya daga cikin yarurrukan da akeyi a kasar. Ya matsa a Savigny-leTemple, a shekarar 1977. Lokacin da yake shekaru 4, Babanshi Joseph Andre Makelele shima dan wasa ne. Ya wakilci Dr Congo, sannan ya karar da rayuwar kwallanshi Division na 3 a gasar kasar Belgium da kungiyar Union Royale Namur.[8]

Ayyukan Kwallo

gyara sashe

A shekaru 15 Makelele yasa hannu a Sporting Melun Dammarie 77. Ya buga kwallan shekara 1, sai ya tashi yana shekaru 16, duk da cewa ya girma a Brest, amma city ce a Nantes inda yasa hannu a matsayin kwararren dan wasa. Nantes ta dauki Makelele a karnin 1992-93 yana dan shekaru 18.

Kungiyar Celta Vigo

gyara sashe

Makelele ya koma Celta Vigo, inda ya share shekaru 2 a kungiyar, inda ya buga kwallo tare da Aleksandr Mostovoi, Valeri Karpin, Haim Revivo da Michel Solgado. Celta Vigo sunyi babbar nasara kamar 4-1 da sukaci Liverpool, da kuma 4-0 da sukayima Juventus a kofin nahiyar turai.[9]

Kungiyar Real Madrid

gyara sashe

Munsan cewa Zidane, Raul da Figo bazasu azu ba, amma ana bukatar wani wanda zai iya yin tare (tsaro).

Ariggo Sacci shi ya bayyana Real Madrid na bukatar dan tsakiya mai tarewa.[10]

Lokacin bazara a shekarar 2000 lokacin da tsohon abokin wasan Makelele a kungiyar Nantes Christian Karembeu ya bar Real Madrid zuwa Middlesbrough FC, sai aka maye gurbinshi da Makelele. Celta Vigo basa san ya tashi har sai anmusu tayi mai gwabi, inda suka yanke €14 million kuma darajar dan wasan bata kai hakaba sai da ajent dinshiyakai lamarin wajen yan sanda, Marc Roger[1][11]

A Real Madrid, Makelele ya kara samun kyaututuka inda ya lashe Laliga guda 2, kofin zakarun nahiyarar turai, Supercopa de Espana, UEFA Super Cup da Intercontinental Cup. Makelele ya tabbatar da kansa a cikin yan tsakiya masu tare mafi kyau a lokacin.[12]

A bazara 2003, Makelele yasanya hannu tare da kungiyar Chelsea akan jumullar kudi €16.8 million. Makelele ya zama dan wasa mai matukar muhimmanci a kungiyar Chelsea.[13]

Chelsea sun gama na 2 a gasar FA Premier League a 2003-04, sannan an korosu a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a hannun kungiyar Monaco a matakin kusa da na karshe.[14]

Biyo bayan korar Ranieri da shigowar Jose Morinho, Makelele ya zama dan wasan da yafi kowa a Chelsea a shekarar 2004-05 inda yaci duka Premier League da kofin lig. Tarenshi shiya ba manyan yan wasan Chelsea irinsu Frank Lampard, Joe Cole, Arjen Robben da Didier Drog a Damascus su nuna kwarewarsu a fili. Jose Morinho ya bayyanar dashi a matsayin dan wasan shekara da yafi kowa a Chelsea.[15]

Paris Saint Germain

gyara sashe

A 18 ga watan Yuli, 2008 aka wallafa labarai cewa Makelele ya kulla yarjejeniya da P. S. G, inda kungiyar Chelsea tayi sanarwar sakin dan wasan.[16][17]

A ranar 25 ga watan Fabrairu 2010, Makelele ya fadi ranar aje kwallo a watan Yuni, saidai ya manta da maganar inda ya kara shekara 1 da P. S. G.[18] ya lashe kofin Coupe de France a shekarar 2009-10 tare da P. S. G inda ya aje ƙwallo a ƙarshen kaka. Anba Makelele mukamin maitaimakin mai horarwa Carlo Ancelotti wand ya koma P. S. G daga tsohuwar kungiyar Makelele wato Chelsea.[2][19]

Rayuwar Kasa

gyara sashe

Makele ya fara buga ma Faransa wasane a karawar da sukayi da Norway a shekarar 1995,[20] sannan yaje ya wakilci Faransa a gasar Olympics wanda akayi a bazarar 1996. Makelele bai cikin wadanda aka dauka a gasar cin kofin duniya da gasar Euro 2000. Ya buga gasar cin kofin duniya na 2002 a wasan rukuni da ya buga da kasar Denmark a karkashin mai horaswa Jacques Santini. Makelele shine zabin farko a gasar Euro 2004 inda ya buga wasanni 4 a jere.[21][22][23]

Makele ya yanke shawarar aje kwallo a ƙasa saboda ya meda hankali a kungiyar Chelsea, wata 11 daya wuce dashi da wasu abokan kwallanshi irinsu Zinedine Zidane da Lilan Thuram su duka suna cikin wadanda ke layin aje kwallo amma suka kara lokaci a karkashin mai horaswa Raymond Domenech wanda yaba Makelele horo tun U21 har yaba Faransa dama ta samu nasarar samun damar cin kofin duniya a Jamus 2006.[24]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Ranked! The 101 greatest football players of the last 25 yebars: full list". FourFourTwo (253 ed.). 13 February 2018. Retrieved 22 December 2023.
  2. 2.0 2.1 Wallace, Sam (24 February 2007). "Doing a Makelele – so good they named it after him". The Independent. London. Archived from the original on 27 November 2010.
  3. "What does a central midfielder do in 2010?". ZonalMarking.net. 30 July 2010. Archived from the original on 29 July 2016. Retrieved 13 July 2016.
  4. "15 years on from Zidane's final wonder goal". UEFA.com. Union of European Football Associations. 15 May 2017. Retrieved 23 September 2018.
  5. "FIFPro World XI: Which 11 players made FIFA's team of the year for 2014?". 13 January 2015
  6. "Claude Makelele returns to Chelsea in a new coaching role". Chelsea F.C. Retrieved 2 August 2019.
  7. Mtembezi, Chumvi (2002). "Swahili Stars". Archived from the original on 18 July 2008. Retrieved 30 November 2008.
  8. Close "À la gloire du père, la saga Makélélé" (in French). Sport Magazine. 19 December 2017. Retrieved 2 August 2019.
  9. "Celta Vigo - Juventus 4:0 (Europa League 1999/2000, Ottavi di finale)". calcio.com (in Italian). Retrieved 12 July 2021.
  10. Wilson, Jonathan (2013). Inverting the Pyramid. Nation Books. ISBN 9781568589633.
  11. "Former Agent Reveals the Shocking Events That Led to Claude Makelele Joining Real Madrid From Celta". 90 Min. 8 October 2017. Retrieved 2 August 2019.
  12. "From Ligue 1 to Superstardom: Claude Makelele - Real Galactico". Goal. 4 February 2017. Retrieved 2 August 2019.
  13. Chelsea 2-2 Monaco". 5 May 2004. Retrieved 29 June 2020.
  14. "Chelsea 2-2 Monaco". 5 May 2004. Retrieved 29 June 2020.
  15. "How Claude Makelele changed English football | Official Site | Chelsea Football Club". ChelseaFC. Retrieved 12 July 2021.
  16. "Makelele leaves Chelsea for PSG". BBC Sport. 21 July 2008. Retrieved 26 January 2019.
  17. "Makélélé leaves Chelsea to link up with PSG". FourFourTwo. Future. Archived from the original on 12 March 2012. Retrieved 21 July 2008.
  18. "Makelele to hang up boots". Sky Sports. 25 February 2010. Archived from the original on 21 October 2013.
  19. "Former France international Claude Makelele to become Carlo Ancelotti's assistant at Paris Saint-Germain - report". goal.com. 30 December 2011. Archived from the original on 6 May 2021.
  20. "Finally Makelele". The Daily Star. Dhaka. 2 September 2003. Archived from the original on 19 August 2014. Retrieved 17 August 2014.
  21. "Zidane strikes stun England as France fight back". UEFA.com. 14 June 2004. Retrieved 27 August 2019.
  22. "Henry makes the difference for France". UEFA.com. 22 June 2004. Retrieved 27 August 2019.
  23. "Slick Greece shock EURO holders France". UEFA.com. 25 June 2004. Retrieved 27 August 2019.
  24. "Zidane and Makelele return to Les Bleus". The Guardian. 3 August 2005. Retrieved 27 August 2019
  NODES
Association 4
INTERN 1