Margaret Thatcher
Margarate Thatcher (1925-2013), shugabar jam'iyyar Conservative daga shekarar alif dari tara da saba'in da tara 1979 zuwa shekara ta alif dari tara da 1990, kuma ita ce mace ta farko da ta zama Firaministan ƙasar Birtaniya kuma ita ce tafi kowanne firaminista dadewa a kan kujerar a karni na ashirin, sannan kuma ta samu nasara a zaɓukan ƙasar har sau uku, wato dai sau uku tana zama Firaministan ƙasar a jere, tun daga shekarar 1979 da shekara ta 1983 da kuma shekarar 1987.[1]
An kuma haifi Margarate Thatcher ne a ranar 13 ga watan Oktoban shekarata 1925 , kuma ta yi Makarantar Firamare na Kesteven da kuma sakandaren 'yan mata ta Grantham da kuma Somerville na jami'ar Oxford.[2]
Kafin kuma ta shiga harkokin siyasa a shekara ta 1959, ta kasance mai bincike na kimiyyar Chemistry daga shekarar 1947-54. A shekarar 1954 ne kuma ta zama cikakkar lauya. Daga shekarar 1970 zuwa 1974 kuma ta zama sakatariyar harkokin ilmi ta Birtaniya.[3]
A zamanin mulkin ta ne dai Rhodesiya ta samu 'yancin kai ta zama Zimbabwe a shekarar 1979. Sai dai wani abu ɗaya da ya ƙara wa Magarate Thatcher farin jin, shi ne nasasar da dakarun Ingila suka samu a lokacin yaƙin tsibirin Falklands a shekarar 1982, abin da ya sa Birtaniyawa suka sake zaɓen ta a zaɓen shekara ta 1983. Gama ka ɗan daga cikin abinda take cewa bayan sarandar da Sojojin Angentina suka yi wanda kuma ya kawo ƙarshen Yaƙin, inda kuma take cewa: Ina son sheda maku sarandar da sojojin Argentina suka yi, wanda ya bai wa Birtaniya nasara a wannan yaƙi na mallakar tsibirin falklands: A shekarar 1990 ne Magarate Thatcher ta sauƙa daga kan muƙamin Firaministan Birtaniya, kuma sunan mijinta Sir Denis Thatcher. Kuma tana da 'ya'ya biyu Sir Marka Thatcher da kuma Hon.[4] Carol Thatcher da jikoki biyu mace da namiji. Yanzu haka dai Madam Thatcher tana da shekaru 84 a duniya.[5]
Hotuna
gyara sashe-
Shugaba Gerald Ford na Conservative Party ke saduwa da Margaret Thatcher a Oval Office
-
Margaret Thatcher
-
Thatcher da Ruud Lubbers
-
Thatcher da wasu shugabannin duniya
-
Thatcher da Lubbers
Manazarta
gyara sashe- ↑ In her foreword to the Conservative manifesto of 1979, she wrote of "a feeling of helplessness, that we are a once great nation that has somehow fallen behind".
- ↑ Winning support from a majority of her party in the first round of votes, Thatcher fell four votes short of the required 15% margin to win the contest outright. Her fall has been characterised as "a rare coup d'état at the top of the British politics: the first since Lloyd George sawed Asquith off at the knees in 1916."
- ↑ She was decidedly cool towards reunification prior to 1990, but made no attempt to block it.
- ↑ Lawson (1992, p. 64) lists the Thatcherite ideals as "a mixture of free markets, financial discipline, firm control over public expenditure, tax cuts, nationalism, 'Victorian values' (of the Samuel Smiles self-help variety), privatisation and a dash of populism".
- ↑ Campbell (2011a, p. 800) also writes about a third view that can be argued: Thatcher "achieved much less" than she and her "dries" would claim; she failed to curb public spending, diminish or privatise the welfare state, change fundamental attitudes of the general public, or "enhance" freedom where she had instead centralised control over "many areas of national life".