Sunday Adeniyi Adegeye (an haife shi a 22 Satumba 1946), anfi saninsa da King Sunny Adé, ya kasance dan' Najeriya ne, mawakin jùjú, marubucin waka kuma mai kide-kide.[1] Ana daukar sa amatsayin n'a farko daga acikin mawakan African pop da suka samu nasara a duniya, kuma ana ganin shi mawakin da yafi a Afrika na kowane lokaci.[2]

Sunny Ade
Rayuwa
Haihuwa Ondo, 22 Satumba 1946 (78 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yaren Yarbawa
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a mawaƙi da conductor (en) Fassara
Artistic movement Kidan Jujú
Kidan Afirka
Kayan kida murya
Jita
Jadawalin Kiɗa I.R.S. Records (en) Fassara
Island Records
IMDb nm0011750
DJA tare da King Sunny Ade
Sunny Ade

Adé ya kafa nashi kamfanin Wakar a 1967, wanda da fari ya kira da African Beats. Bayan nasarori a Najeriya a shekarun 1970s da kafa tashi independent label, Adé ya sanya hannu da Island Records a 1982 kuma ya samu nasara a duniya da fitar da albums Juju Music (1982) da kuma Synchro System (1983); na karshen tasa yasamu gabatarwa a Grammy, na farko da wani daga Najeriya ya fara samu. A 1998 album dinsa Odu itama ta samar masa da gabatarwa a Grammy. Adé ayanzu yana rike ne da mukamin Babban Shugaba na Musical Copyright Society of Nigeria.

Manazarta

gyara sashe
  1. "King Sunny Ade: Juju legend launches radio station". Pulse News. Retrieved 3 November 2019.
  2. Gini Gorlinski, The 100 Most Influential Musicians of All Time 08033994793.ABA, Publisher: Rosen Education Service (January 2010)
  NODES