Ummu Kulthum bint Muhammad

Yar Annabi,

 

Ummu Kulthum bint Muhammad
Rayuwa
Haihuwa Makkah, 603 (Gregorian)
Mutuwa Madinah, 10 Disamba 630
Makwanci Al-Baqi'
Ƴan uwa
Mahaifi Muhammad
Mahaifiya Khadija Yar Khuwailid
Abokiyar zama Utaybah bin Abu Lahab (en) Fassara
Sayyadina Usman dan Affan  (624 -
Ahali Rukayyah, Fatima, Zainab yar Muhammad, Abdullahi ɗan Muhammad, Ibrahim ɗan Muhammad da Yaran Annabi
Sana'a
Sana'a Matar aure
Imani
Addini Musulunci

Umm Kulthūm bint Muḥammad ( Larabci: أم كلثوم بنت محمد‎ ) ( c. 603 zuwa 630) ta kasance ‘yar Annabi Muhammadu ta uku a mata, a wurin matarsa ta farko Khadija bint Khuwaylid .

Musulunta

gyara sashe

An haife ta a Makka, mai yiyuwa ita ce ta biyar a cikin 'ya'yansu shida. [1] :10An ɗaura mata aure a shari'ance kafin watan Agusta shekara ta 610 ga Utaybah ibn Abi Lahab, amma ba a take auren ba. [1] :26[2] :163Ta kasance tana zaune tare da iyayenta lokacin da Muhammadu ya fara ayyana kansa a matsayin annabi, kuma Umm Kulthum ta musulunta jim kaɗan bayan mahaifiyarta ta yi. [1] :26

Bayan Muhammadu ya gargadi Abu Lahab kan wutan jahannama a shekara ta 613, Abu Lahab ya gaya wa Utaybah cewa ba zai sake magana da shi ba, har sai dai in ya saki Ummu Kulthum, don haka sai ya yi. [1] :26Dan uwanta na wurin uwa mai suna Hind ibn Abi Hala ya tambayi Muhammad, me ya sa ka raba Ummu Kulthum da Utaybah? Muhammad ya amsa da cewa, Allah bai bar ni in aurar da ita ga wanda ba zai shiga Aljanna ba. [3]

Muhammad ya bar Makka a watan Satumba shekara ta 622. Ba da dadewa ba Zaidu bn Haritha ya kawo wa Ummu Kulthum da 'yar uwarta Fatima umarnin su bi babansu Madina . [2] :171–172Baffansu Al-Abbas ya dora su akan rakumi; amma suna tafiya sai Huwayrith bn Nuqaydh ya buge dabbar soboda ta jefar da su a kasa. [4] :773Sai dai Ummu Kulthum da Fatima sun isa Madina lafiya. [1] :26[2] :163Muhammad ya tuna da harin kuma, lokacin da ya yi nasara a Makka a shekarar 630, ya yanke wa Huwayrith hukuncin kisa. [5] :551

Aure na biyu

gyara sashe

Bayan rasuwar 'yar uwarta Ruqayya ta bar Uthman a mai takaba, sai ya auri Ummu Kulthum. An ɗaura auren bisa doka a watan Agusta/Satumba shekara ta 624, [6] :128[2] :163amma ba su zauna tare ba sai Disamba. Auren basu haihu ba. [1] :26[2] :163

A shekarar 650 'yan tawaye sun fito a jihohin Masar da Iraki. A shekara ta 655 wasu gungun miyagu na Masar sun yi tattaki zuwa Madina, wurin zama na hukumar khalifa. Usman kuwa ya kasance mai sulhuntawa, sai ‘yan tawayen suka koma Masar. Amma ba da dadewa ba, wasu gungun 'yan tawaye suka yiwa Usman kewaye a gidansa, kuma bayan an shafe kwanaki da dama ana gwabza faɗa, aka kashe shi.

Ummu Kulthum ta rasu a watan Nuwamba/Disamba shekara ta 630. [1] :26[2] :11,163Mahaifinta ya yi sallar jana'izarta cikin hawaye; sai Ali da Usama bn Zaid da Abu Talha suka ajiye gawar. [1] :27[2] :11–12,163Muhammad ya ce, da ina da 'ya'ya mata guda goma, da na aurar da su duka ga Usman. [1] :26An san Uthman da Dhu al-Nurayn ("Ma'abucin fitilu biyu") domin an yi imani da cewa babu wani mutum da ya taɓa auren 'ya'ya mata biyu na Annabi. [7] :369

Ra'ayin Shi'a goma sha biyu

gyara sashe

Bayanan ‘ yan Shi’a na baya-bayan nan ba su dauke ta a matsayin ‘yar Muhammadu ta gaskiya ba; suna daukar Fatima kaɗai a matsayin diyarsa tilo. A wajen mafi yawan ‘yan Shi’a da Ahlus-Sunnah, ruwayoyin da suka tabbatar da haka ba su inganta ba. [8] [9]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 1.7 1.8 Muhammad ibn Saad. Kitab al-Tabaqat al-Kabir vol. 8. Translated by Bewley, A. (1995). The Women of Madina. London: Ta-Ha Publishers.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 2.6 Muhammad ibn Jarir al-Tabari. Tarikh al-Rusul wa'l-Muluk. Translated by Landau-Tasseron, E. (1998). Volume 39: Biographies of the Prophet's Companions and Their Successors. Albany: State University of New York Press.
  3. Ibn Hajar al-Asqalani, Al-Isaba vol. 6 #9013.
  4. Abdulmalik ibn Hisham. Notes to Ibn Hisham's Life of Muhammad. Translated by Guillaume, A. (1955). The Life of Muhammad. Oxford: Oxford University Press.
  5. Muhammad ibn Ishaq. The Life of Muhammad. Guillaume, A. (1955). The Life of Muhammad. Oxford: Oxford University Press.
  6. Muhammad ibn Jarir al-Tabari. Tarikh al-Rusul wa'l-Muluk. Translated by Poonawala, I. K. (1990). Volume 9: The Last Years of the Prophet. Albany: State University of New York Press.
  7. Ismail ibn Umar ibn Kathir. Al-Sira al-Nabawiyya. Translated by Le Gassick, T. (1998). The Life of the Prophet Muhammad, vol. 2. Reading, U.K.: Garnet Publishing.
  8. Yasin T. al-Jibouri (1994), Khadija Daughter of Khuwaylid Error in Webarchive template: Empty url.
  9. Ordoni, Abu Muhammad; Muhammad Kazim Qazwini (1992), Fatima the Gracious, Ansariyan Publications. ISBN B000BWQ7N6
  NODES
Note 1