Zogale ko Zogala (Moringa oleifera) nau'ine a cikin nau'in ganye wanda kuma akan sarrafa shi wajan yin magani, miya kwado da sauransu. Zogale na iya girma ya kai tsayin bishiya, amma a ainihin tsarin "daga tsirrai na duniya" (ICBN), yawancin zogale ba bishiya ba ce.

Zogale
Conservation status

Least Concern (en) Fassara  (IUCN 3.1)
Scientific classification
KingdomPlantae
OrderBrassicales (en) Brassicales
DangiMoringaceae (en) Moringaceae
GenusMoringa (en) Moringa
jinsi Moringa oleifera
Lamarck, 1785
General information
Tsatso ben oil (en) Fassara, Moringa oleifera extract (en) Fassara, Moringa oleifera fruit (en) Fassara da Moringa oleifera seed (en) Fassara
Zogale
Dafaffen zogale
ƴaƴan zogale kore shar
ganyen zogale da furenta
garin zogale
kanzogale
'ya'yan zogale
Zogale
Zogale

Shi tushen zogale yana daya daga cikin tsirran da Allah Ya yi wa albarka kasancewar bincike-binciken kimiyya ya tabbatar da cewa yana da amfani a fannoni da dama na inganta lafiyar Dan'adam. Zogale yana kuma kumshe da sinadaran dake warkar da cututtuka kamar ciwon suga, hawan jini, da kuma yawancin cututtukan da wasu irin kwayoyin halittu wadanda idon mutum baya iya ganinsu (in ba tare da na'urar kambama qananan halittu ba) suke sabbabawa. A saboda haka, kamar yadda yawancin jama'a suka sani, cin zogale da yin miyar sa da shan shayin shi, hadi da shan ruwan shi, cikin yardar Allah, zai yi sanadiyyar samun waraka daga cututtukan da aka ambata a sama, dama wasu wadanda ba a ambata ba. Zogale yana Kara lafiyan jiki sosai, yana kuma daga cikin nau'in abincin da masu shekaru 40 zuwa sama ya kuma kamata su rika amfani da shi.

Amfanin Zogale

gyara sashe
  • Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).
  • Ana kuma shafa danyen ganyen zogale a kan goshi domin maganin ciwon kai.
  • Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale insha Allah jinin zai tsaya.
  • Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.
  • Ana sanya garin zogale a kan wani rauni ko gembo domin sauri warkewa.
  • Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma kara wa mutum kuzari.
  • Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon shawara.
  • Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.
  • Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.
  • Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.
  • Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi.
  • Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.
  • Ana daka ganyen zogale da ‘ya’yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.
  • Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya ‘ya’yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.
  • A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karin karfin da namiji da sa masa kuzari, haka kuma yana Kara wa mata nishadi.
  • A daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).
  • Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon AIDS zogale na rage radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.
  • Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.
  • Yana da Kuma sauran amfani
  • Ana dafa danyen zogale a kwadanta da kuli-kuli aci.[1]

Manazarta

gyara sashe
  1. Idris, Aisha (3 October 2021). "Abinci da ya kamata ku ci idan kun haura shekara 40 a duniya". BBC Hausa.Com. Retrieved 3 October 2021.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
  NODES